Zazzabin Lasa ya Hallaka Mutane 29 ya Kuma Kwantar da 195 a Jjihohi 11 na Najeriya–NCDC.

Zazzabin Lasa ya Hallaka Mutane 29 ya Kuma Kwantar da 195 a Jjihohi 11 na Najeriya–NCDC.

Daga Kabiru Yusuf, Abuja

Cibiyar shawo kan yaduwar cututtuka ta Najeriya ta bayyana cewa akalla mutane 29 ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da zazzabin cutar Lasa yayin da kuma Zazzabin ya kwantar da wasu 195 a jihohin Najeriya 11.

Babban Darakta a cibiyar hana yaduwar cutttutukan, Dr Chikwe Ihekweazu, wanda ya tabbatar da hakan ya ce wannan kididdigar an fitar da ita  ne ranar juma’a 24/01/2020.

A cewar babban Daraktan, kididdigar ta nuna cewar, an samu kashi 89 na bullar matsalar ne a jihohin Ondo, Edo da kuna Ebonyi inda cibiyar ta danganta karuwar yaduwar cutar da matsalolin yanayi.


A wani yunkuri na shawo kan matsalar a cewar babban Daraktan, gwamnatin ta bude wata cibiya ta bada taimakon gaugawa ranar juma’ar data gabata wadda zata ringa kulawa da yadda ayyuka ke gudana. 

Cibiyar, Kamar yadda daraktan ke cewa, zata ci gaba da taimakawa jihohin wajen kokarin da suke na shawo kan wannan cuta, inda ya kara da cewa a cikin makwanni da suka gabata, cibiyar ta tura jami’anta jihohin 5 da aka samu bullar wannan cuta.

Bayanan da suka fiti daga cibiyar sun nuna cewar, an samu raguwar yaduwar Zazzabi daga kashi 23.4 da ake da shi a shekara 2019 zuwa kashi 14.8 da ake da shi a wannan sabuwar shekarar.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0