Zan Rage Kudin Aikin Hajji don Ya Yi Tsada….Inji Sabon Shugaban NAHCON

Zan Rage Kudin Aikin Hajji don Ya Yi Tsada….Inji Sabon Shugaban NAHCON

Daga Mahmood Sadeeq

Sabon shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriya Barrister Zikirullah Hassan  ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da ya rage kudin aikin Hajji a Najerya da zarar ya kama aiki.

Barrister Zikirullah ya sanar da hakan ne a lokacin da ‘yan majalisar datawan Najeriya suka tantance shi da sauran mabobin hukumar a Abuja.

Batun kudin aikin Hajji da ke kara tsada a Najeriya babban kalubale ne, a bara mahajattan da suka biya ta gwamnati sun bada Naira milyan daya da rabi, N1.5 yayainda na jirgin yawo sun biya kasa da haka.

Wa’adin Aikin Haji ga ‘Yan Najeriya

Sabon shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriya ya yi alkawarin zai duba yawa ko adadin kwanakin da mahajattan Najeriya ke yi a kasa mai tsarki domin aikin Hajji.

‘’Ana daukar kwanaki biyar zuwa shida ne a aikin Hajji, amma kuma ana sanya ‘yan Najeriya su kwashe kusan kwana 40 a kasar Saudiyya’’. Inji sabon shugaban hukumar aikin Hajjin

Nasan abu ne da ba a karkashin ikonmu yake ba, amma dole ne mu nemo hanyar da zamu rage yawan kwanakin da mahajatta ke yi a kasar Sudiyya.

Shugaban kwamitin kula da aikin Hajji a majalisar datawan Najeriya Sanata Adamu Bulkachuwa yace ‘yan majalisar zasu sanya idannu sosai a kan aiyyukan hukumar domin su taimaka mata ta inganta aiyyukanta.

Idan za’a tuna a ranar 3 ga watan Disambar 2019 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar da sunayen mambobin hukumar da sabon shugaban a majalisa domin amincewarta.

A yanzu abinda ya rage sai kama aiki ga sabon shugaban hukumar a dai dai lokacin da ake kusantar aikin Hajjin bana.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0