‘Yan Sanda sun Hana Kowa Shiga Sakatariyar APC dake Abuja.

‘Yan Sanda sun Hana Kowa Shiga Sakatariyar APC dake Abuja.

Daga Mohammed Lawal   :

Jiya Juma’a ne Supeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, ya ja  kunnnen shugabannin jam’iyar ta APC da suke kai ruwa rana dangane da shugabancin jam’iyyar, da su kauracewa sakatariyar jam’iyyar ta APC dake Abuja.

 Jami’an hukumar DSS da na rundunar ‘yan sanda sun hada karfi wajen tabbatar da doka da oda a harabar sakatariyar jam’iyyar ta APC tare da hana kowa shiga cikin sakatariyar. Tuni dama aka garkame sakatariyar.

 Supeto janar na ‘yan sandan ya gana da bangarorin biyu masu takaddama da juna ranar juma’a inda ya ja kunne kowanensu da ya guji daukar doka a hannunsa.

 Ranar laraba ne bangaren dake adawa da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole suka samu oda daga wata kotun tarayya dake Abuja, wadda ta haramtawa Oshiomhole kiran kansa a matsayin shugaban jam’iyyar ta APC.

Sanar da wannan hukunci ke da wuya sai aka tura jami’an tsaro  zuwa harabar sakatariyar domin bayar da tsaro.

‘Yan jarida ne da wasu daga cikin ma’aikatan sakatariyar aka baiwa damar shiga cikin harabar, yayin da wasu ma’aikatan masu yiwa Oshiomhole hidima aka hana su shiga cikin sakatariyar. Kazalika suma membobin jam’iyyar ta APC da baki ba’a bari su kusanci sakatariyar.

 To saidai wan shekaren bayar da wannan hukunci da kotun Abuja tayi na dakatar da Oshiomhole daga shugabancin jam’iyyar, sai kuma wata kotun tarayya a Kano ta bada hukuncin dakatar da yin aiki da hukuncin kotun ta Abuja.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0