‘Yan sanda a Katsina sun cafke masu garkuwa da mutane su 5.

‘Yan sanda a Katsina sun cafke masu garkuwa da mutane su 5.

Daga Mohammed Lawal:

Rundunar ;yan sanda ta musamman kan yaki da ‘yan fashi a Katsina ta dakile wani yunkurin da masu garkuwa da mutane su shidda sukayi na karbar kudin fansa har naira miliyan 15 daga hannun mata matar aure mai suna Hajiya Habiba.

Biyar daga cikin mutanen tuni suna hannu,harma an jefa kurkuku, yayin da na shiddan mai suna Adda’u Lawal ya samu arcewa, ko da yake ‘yan sandan suna can suna farautar shi.

An gano cewa mutanen su shidda sun afka gidan Hajiya Habiba a kauyen ‘Yar ilyau, inda suka yi mata fashin kudi har naira dubu 52 da dari 7, bayan sun yi mata fashin kuma suka yi awon gaba da ita.  

Da farko dai mutanen sun fara kai Hajiya Habiba ‘yar shekaru 65 cikin daji, sannan daga bisani suka kai ta wani gida  a kauyen ‘Yar gamji a karamar hukumar Batagarawa, suka boye ta.  Daga nanne suka fara tuntubar danginta inda suka nemi a basu Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.

Amma ‘yan sanda sun samu nasarar kutsa kai a cikin gidan  da ake tsare da Habiba inda suka kubutar da ita, sannan suka cafke mutane ukku nan take.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0