‘Yan Sanda a Katsina na Farautar Wadanda Suka Tada Bore kan Hana Sallar Juma’a.

‘Yan Sanda a Katsina na Farautar Wadanda Suka Tada Bore kan Hana Sallar Juma’a.

Daga Mohammed Lawal :

Matasa da magidanta a garin Kusada dake jihar Katsina sun arce daga gidajensu biyo bayan tarzomar da ta barke ranar asabar akan hana taron sallar Juma’a da mahukunta suka yi, abinda yayi sanadiyyar tada boren da ya haddasa mutuwar mutun daya, tare da kone ofishin ‘yan sanda da gidajen ‘yan sanda da motoci bakwai da Babura goma.

Yanzu daukacin shaguna da gidaje sun kasance kulle, yayin da kan titunan garin babu kowa. Yayin da ‘yan sanda suke ci gaba da farautar wadanda suke da hannu kan wannan danyen aiki.

Rahotanni sun bayyana cewa mata ne da kananan yara suka rage a garin, maza kuwa sai tsofaffi da gajiyayyu da marasa lafiya suka rage.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba, yayi nuni da cewa akwai mutane da dama da a halin yanzu suke a hannun ‘yan sanda, amma kuma ya kara da cewa duk wanda aka samu baya da hannu a cikin wannan ta’asa za’a sake shi. Su kuma wadanda suke da hannu kuma suka arce za’a ci gaba da farautarsu.

 Ranar 27 ga watan Maris ne gwamna Aminu Bello Masari ya sanar da sanya haramci kan duk wasu taruka na addini, wanda ya hada da hana sallar Juma’a da kuma taron coci ranar lahadi gami da manyan tarukan aure a matsayin matakin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Amma duk da wannan haramcin taron sallar Juma’ar sai da liman Malam Hassan ya jagoranci sallar juma’a a garin na Kusada, abinda ya sanya ‘yan sanda suka yi awon gaba dashi zuwa chaji ofis na ‘yan sanda dake Malumfashi domin amsa tambayoyi.

Wannan lamari na kama Limamin juma’ar ya harzuka al’ummar garin suka dauki a doka a hannun su, suka tada bore tare da kone kone.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0