‘Yan sanda a Hong Kong sun yi taho mu gama da masu zanga zanga.

‘Yan sanda a Hong Kong sun yi taho mu gama da masu zanga zanga.

Daga Mohammed Lawal

‘Yan sanda a Hong Kong sun fesawa dubban masu zanga zanga hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su bayan da suka gudanar da wani taron gangami ranar asabar din nan 13 ga watan Yuli, 2019. 

‘Yan sandan ruwan zafi

Masu zanga zangar dai sunyi taho mugama da ‘yan sandan a Sheng Shui domin ci gaba da nuna adawarsu da Beijing dangane  dokar nan da zata baiwa Beijing damar hukunta wanda ya aikata laifi a Hong Kong.

Shugabar yankin na Hong Kong Carrie Lam ta jingine wannan shirin doka har sai abinda hali yayi, amma wannan mataki bai gamsar da masu zanga zangar ba, Abinda suke bukata shine soke dokar kwata kwata.

Masu zanga zangar dai wadanda yawansu ya kai dubu 30 suna bukatar ganin Carrie Lam ta sauka daga mukaminta   

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0