Yan matan Chibok: Buhari yace har yanzu akwai fatan ceto su

Yan matan Chibok: Buhari yace har yanzu akwai fatan ceto su

Daga Mahmood Sadeeq

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tunatar da iyayen ‘yan matan Chibok da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram suka sace shekaru biyar kenan cur, cewa, gwamnati bata manta da ‘ya’yansu ba.

A ranar 14 ga watan   Afrilun shekara ta 2014 ne ‘ya’yan kungiyar Boko Haram suka afka makaratar sakandare ta Chibo inda suka sace ‘yan mata 276.

Kakakin yada labaru na shugaban Najeriyar Garba Shehu wanda ya fitar da sanarwa yace, shugaba Buhari ya yiwa iyayen yaran alkawari a lokacin da ya gana da su farkon mulkinsa  cewa, zai tabbatar da dawo da yayan nasu.

‘’Yana sane da alkawarin da y a yi, kuma wannan ne ya sanya alummar Chibok suka bashi kuri’a sosai a zaben da aka yi a watan Febrairu. Ya zuwa yanzu gwamnatin shugaba Buhari ta samu nasarar ceto ‘yan mata 107, shugaba kasa ba zai sarara ba har sai ya ceto sauran daukacin ‘yan matan don mika su ga iyayensu’’.

Mallam Garba Shehu ya kara da cewa gwamnati na  iyakar kokari domin ceto ‘yan matan Chibok da Boko Haram ke rike da su har da Leah Sharibu wadda ita ma a ranar 19 ga watan Febrairu ‘yan Boko Haram suka sace ta daga makarantar sakandare ta Dapchi da ke jihar Yobe.

Shekaru biyar kenan dai da sace ‘yan matan na Chibok. Kungiyar Bring Back Our Girls da ke fafutuka na ganin an sako ‘yan matan tace ba zata ja da baya ba, har sai an sako daukacin ‘yan matan da ke hanun Boko Haram.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0