‘Yan bindiga sun kai  harin ramuwar gayya a jihar Katsina, sun kashe mutane 36.

‘Yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a jihar Katsina, sun kashe mutane 36.

Mutane da dama ne suka rasa rayukan su sakamakon wani harin ramuwar gayya da ‘yan bindiga suka kaiwa  al’ummar kauyen Tsamiyar Jino dake karamar hukumar Kankara jihar Katsina.  Wannan hari ya biyo bayan wani artabu da aka yi tsakanin  ‘yan bindigar da ‘yan sintiri. ‘Yan sintirin sun kai harin ga ‘yan bindigar  a kasuwar kauyen ranar lahadi, inda suka samu nasarar bindige wani daya daga cikin jiga jigan ‘yan bindigar wanda ake kira da ‘Baban kusa’ har lahira.

Yayin da ‘yan bindigar dake zaune cikin daji suka samu   labarin kisan daya daga cikin shugabannin nasu , sai suka kawo farmakin ramuwar gayya dauke da muggan makamai  a kan ‘yan kauyen, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, suka hallaka mutane da dama. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa kimanin mutane 38 ne ‘yan bindigar suka kashe.

 Mai garin Tsamiyar Jino Jaafaru Bello Jino,wanda ya tabbatar da faruwar lamarin,  ya bayyana kisan da aka yi wa yan garin nasa a matsayin babbar masifa. Ya kara da cewa gawarwakin mutanen da aka hallaka suna can warwatse cikin gonaki, suna jin tsoron zuwa kwaso su domin a yi masu jana’iza.

Biyo bayan wannan lamari ne ranar litinin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta tura daruruwan ‘yan sanda zuwa kananan hukumomin takwas da ake da matsalar tsaro a jihar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0