Yadda na taimakawa mahaifiyata muka kashe  mahaifina.

Yadda na taimakawa mahaifiyata muka kashe mahaifina.

Kabiru Yusuf

Hukumar ‘yan Sanda ta jihar Niger ta kama wani dan shekarar 25 mai suna Babangida Usman da mahaifiyarsa Hafsat Alitu bisa zarginsu da ake da kashe mahaifinsa, Ali Haruna.

Kamar yadda Jaridar The Nation ta rawaito, Madam Hafsat Aliyu da Mijinta Aliyu Haruna sun samu sabani a tsakaninsu, inda fada ya kaure a tsakaninsu. Ko da zuwan dan su Usman sai ya shiga fadan da nufin tare wa mahaifiyarsa, inda suka yi wa mahaifin nasa dan shekarar 60 da haihuwa dan karen duka, har suka kashe shi.

Lamarin ya faru ne a wata unguwa dake bayan makarantar Firamaren Shango a karamar hukumar Chanchaga, dangane da wani sabani kan ‘Yarsu da ake Zargin ta saci kudin mahaifiyarta

Kamar yadda rahotan ya nuna, mahaifin ya yi kokarin kare ‘yar daga zargin da ake yi wa ‘yar tasu, lamarin da ya kai su ga kokawa.

Da jin labarin iyayensa na fada, Usman bai yi wata-wata ba da zuwan sa gidan Sai kawai ya shiga cikin fadan da nufin tare wa mahaifiyarsa, inda suka yi wa mahaifinsa dukan kawo wuka kafin makwabta su karbe shi. 

Ko da aka kai Malam Haruna asibitin kwararru na Ibrahim Badamasi Babangidan, sai Harunan ya ce ga garinku nan.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Usman ya ce ya shiga fadan ne da nufin ceton mahaifiyarsa, ba tare da sanin yin hakan zai ita kai wa ga rasuwar mahaifin nasa ba..

Da aka tuntubi, jami’in hudda da jama’a na hukumar ‘yan Sandan jihar, Muhammad Abubakar, ya tabbatar da faruwar hakan, inda ya kara da cewa wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake yi masa.  Jami’in ‘yan Sandan ya ce, da zarar hukumar su

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0