Yadda Haramcin Bada Visar   Zai Shafi  ‘Yan Najeriya

Yadda Haramcin Bada Visar Zai Shafi ‘Yan Najeriya

Daga Mahmood Sadeeq

Matakin da shugaban kasar Amurka Donald Truymp ya dauka na san ya sunan Najeriya a jerin kasashe 6 da ya fadada haramcin hana basu takardar visa ya sanya maida murtani mai zafi.

Yan Najeriya da ke son zuwa  su tare a Amurka ne wannan haramci ya shafa, domin sauran ‘yan kasar da ke son ziyara ta yawan shakatawa, da jami’an gwamnati abin bai shafe su ba.

To sai dai Najeriya ce abin zai fi shafar al’ummarta, domin yawan ‘yan Najeriya da suka nemi izinin  shiga Amurka a bara sun ninka yawan na sauran kasashen guda biyar.

Sauran kasashen sune na  Eriteria, Sudan, Tanzania, Kyrgyzstan da kuma Mynamar, a kasashen nan babu wadda dokar zata shafa irin Najeriya.

Muratnin Gwamnatin Najeriya a Kan Haramcin

Tuni daiu gwamnatin Najeriya ta sanar da kafa kwamitin da zai duba wannan haramcin da Amurikan ta sanar.

Shi kansa tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fito fili ya nuna takaicinsa  a kan lamarin.

Kungiyar ‘yan Najeriya da ke Amurka ta bukaci shugaban ya janye sunan Najeriya a kan wannan harumci, domin a cewarsu lamari ne da zai shafi ‘yan kasa a dai – dai lokacin da suke fama da matsaloli na rashin tsaro.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0