Wasu Mazaje a Uganda na Tilastawa Matansu Shayar dasu Mama.

Wasu Mazaje a Uganda na Tilastawa Matansu Shayar dasu Mama.

Daga Mohammed Lawal

Tabi’ar nan ta mazaje masu tilastawa matansu shayar da su mama, musamma ga matan da suke da sabuwar haihuwa, ta zama ruwan dare a wasu sassa na kasashen Tanzania, Kenya da Uganda.

Yanzu haka dai wannan tabi’a ana danganta ta da cin zarafin mata da tursasawa, sannan kuma akwai damuwa dangane da illar da wannan tabi’a zata haifar ga jarirai, musamman sabuwar haihuwa, kamar yadda jaridar Guardian ta UK ta bada rahoto.

 A shekara ta 2018 ne wannan tabi’a ta bayyana a Uganda, yayin da ministar lafiya ta Uganda, Sarah Opendi ta fasa kwai a majalisar dokokin kasar, dangane da wannan tabi’a ta shan nono da mazaje ke yi.

Ministar tayi gargadin dangane matsalar dake tattare da wannan tabi’a musamman ga mata masu shayarwa da kuma su kansu jariran.

 Masana halayyar dan adam sun gudanar da bincike  a gundumar Buikwe dake tsakiyar lardin Uganda, inda a can ne wannan tabi’a ta fi zama ruwan dare, kan dalilin da ke sanya mazajen tursasawa matan nasu da su shayar dasu nono.  

Sakamakon binciken ya nuna cewa sannu a hankali wannan tabi’a ta samu karbuwa, inda wasu mazajen su kan sha maman kafin jariri ya sha, wasu sukan sha sau daya a rana, wasu kuma fiye da haka.

Wasu mazajen sun bayyana cewa idan suka sha nonon sukan samu karfin jiki, sannan kuma yana kawar masu da gajiya. Yayin da wasu kuma suka bayyana cewa nonon yana maganin cututtuka iri iri, daga cikinsu kuwa har yana maganin cutar Sida, ko AIDS.

Matan da damansu sun bayyana cewa tilasta su mazajen keyi, idan kuma suka ki amincewa zata kai ga mazajen suna dukansu. Wasu matan kuma sukace sun tsoron kada mijin nasu ya tafi ga wasu matan, don haka tilas suke biyayya.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0