Tsohon Shugaban Kasar Egypt, Hosni Mubarak, ya Rasu.

Tsohon Shugaban Kasar Egypt, Hosni Mubarak, ya Rasu.

Daga Mohammed Lawal  :

Allah ya yiwa tsohon shugaban kasa Masar, wato Egypt rasuwa ranar Talatar nan, 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2020, a wani asibitin sojoji a birnin Alqahira.

Wani gidan talbijin na gwamnatin Masar ne ya sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar dan shekaru 91 a duniya, wanda ya kwashe tsawon shekaru 30 yana shugaban Masar, tun bayan kisan da aka yiwa Anwar Sadat a shekarar 1981.

Sojoji sun hambarar da gwamnatin Mubarak ne a watan Janairun shekarar 2011, bayan an kwashe tsawon makon ukku ana zanga zangar game gari a kasar.

Tun Lokacin da aka hambarar da gwamnatin Mubarak ne ya shiga cikin halin rashin koshin lafiya, har ta kai ga an kwantar dashi asibiti, inda yayi jiyya har zuwa lokacin da rai yayi halinsa.

Bayan an hambarar da gwamnatinsa, Mubarak ya fuskanci tuhume tuhume da dama da suka hada da cin hanci da kuma kisan masu zanga zangar neman sauyin gwamnati, inda daga bisani kotu ta wankesa bayan an kwashe tsawon lokaci an tafka shari’a.

 Tsohon shugaban kasar, marigayi Mubarak, ya sha tsallake rijiya da baya daga hare haren da aka kai masa da nufin hallaka shi, daga cikinsu kuwa har da harin da aka kaima masa a birnin Addis Ababa na Kasar Habasha a lokacin da ya kai ziyara a kasar a shekarar 1995.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0