Tsohon Sarki Kano Yayi Jawabi Mai Sosa Rai.

Tsohon Sarki Kano Yayi Jawabi Mai Sosa Rai.

Daga Mohammed Lawal  :

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamidu Sanusi ya maida martini dangane da tsigewar da gwamnatin jihar Kano tayi masa a jiya litinin. Yayi jawabi mai sosa rai, inda ya fara da cewa “Ko da yaushe muna fada cewa Sarauta ajaline da ita, kwanukan da Allah ya rubuta a kan gado kayyadaddune. Idan ranakun nan sun zo ko ana so ko ba’a so sai an tafi..Sabo da haka mu mun karbi duk abinda Allah yayi, mun yadda, mun gode, mun yi farin ciki, kuma mun san shine alheri a garemu”

“Karagar sarauta ba abune mai dorewa ba har abada, ya kamata ko wane shugaba ya san da haka. Idan da abune mai dorewa, bazan taba zama sarkin Kano ba. Domin kuwa kafin na hau karagar mulkin akwai wani gabani na, shima akwai wani kafin sa. Sabo da haka babu wani abun damuwa ko makaki.

 “Da zaran wa’adinka ya kare, idan ba ka bar masarautarba da kafafunka, to jama’a zasu fitar da gawarka. Babban abinda ke da mahimmanci she a gama lafiya. Don haka muna godiya ga jama’ar Kano a tsawon shekarun nan bisa ga kauna da soyayya da biyayya da addu’a da suka  nuna mana. Don haka muna kira ga jama’ar Kano da su zauna lafiya da juna.

 “Kuma duk wanda Allah yaba wannan Sarauta, mun umurci iyalan mu da ‘ya’yan mu da wadanda muke da iko akansu da suje suyi masa mubayi’a, su bishi, su kare martabarsa su kare mutuncinsa. Saboda martabarsa da mutuncinsa itace martabar wannan gida.

“Muna godewa ‘yan uwa, muna basu hakuri, muna tabbatar masu cewa Allah baya kuskure, duk abinda Allah yayi shine dai dai.Allah ya sa muyi karshe mai kyau, Allah ya sa mu gama lafiya. Mun gode.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0