Takaddama kan wurin da za’a binne gawar Mugabe.

Takaddama kan wurin da za’a binne gawar Mugabe.

Daga Mohammed Lawal

Takaddama ta kunno kai tsakanin iyalan marigayi Robert Mugabe da kuma gwamnatin kasar dangane da inda za’a binne gawar marigayin..

To sai dai ja in ja tsakanin gwamnati da iyalan Mugabe  dangane da wurin da za’a binnesa zata kawo cikas ga bukin jana’izar marigayin.

Su dai iyalan na Mugabe sun tsaya kai da fata cewa a mahaifarsa , wato kauyen Kutama ne za’a binnesa ranar lahadi, yayin da ita kuma gwamnati ta ce ita ke da alhakin yiwa Mugabe jana’iza,kuma itace zata yanke shawarar inda za’a binnesa.

Don haka gwamnati ta yanke shawarar binne gawar Mugabe a makabartar da ake binne gwarajen mutane na kasar. A cewar iyalan marigayin,wannan shawara da gwamnati ta dauka tayi matukar basu mamaki, domin kuwa ba’a tuntubesu ba kafin yanke wannan shawara.

Yanzu haka dai dubban jama’ane suke yin turuwa cikin dogayen layi domin yiwa marigayi Mugabe kallon karshe, wanda aka ajiye gawar tasa a filin kwallon Rufaro dake birnin Harare.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0