Sama da ‘yan bindiga 300 sun afkawa wani kauye a Katsina a matsayin ramuwar gayya.

Sama da ‘yan bindiga 300 sun afkawa wani kauye a Katsina a matsayin ramuwar gayya.

Daga Mohammed Lawal

Sama da ‘yan bindiga 300 ne bisa babura suka kai farmaki a kan wasu al’umma na kauyen Kirtawa a karamar hukumar Safana jihar Katsina, inda suka hallaka akalla mutane 10 tare da lalata motar ‘yan sanda, a matsayin wani harin ramuwar gayya.

Da yammacin jiya asabar ne 13 ga wannan wata na Yuli ‘yan bindigar suka afkawa wannan kauye dauke da muggan makamai inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi suka kashe akalla mutane goma

Sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ta bayyana cewa da misalin karfe biyar da minti ashirin ne wadannan ‘yan bindiga suka kai wannan mummunan farmaki a kan al’ummar wannan kauye na Kirtawa.

Babban jami’in ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Safana wanda ya jagoranci rundunar tsaro ta Sharan Daji zuwa wannan kauye, ya bayyana cewa sunyi musayar wuta da ‘yan bindigar inda ‘yan bindigar suka harbi tayar motar sulke ta ‘yan sanda, suka kuma raunata wani jami’in rundunar soja da na rundunar tsaro ta fararen kaya.

Yayin da aka kara tura jami’an tsaron zuwa wurin da aka kai wannan hari har ‘yan bindigar sun ranta na kare zuwa cikin daji. ‘Yan bindigar sun bankawa wasu motoci hudu tare da babura biyar wuta, sannan kuma suka yi awon gaba da shanu da ba a san adadinsu ba

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0