Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Katsina ta Cafke wani Gurgu a Dutsinma mai Garkuwa da Mutane.

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Katsina ta Cafke wani Gurgu a Dutsinma mai Garkuwa da Mutane.

Daga Mohammed Lawal :

Biyo bayan bayanan sirrin da ta samu, rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta samu nasarar cafke wani gurgu mai suna Shamsu Lawal   Gurgu  dan shekaru 35 dake kauyen ‘Yaryadiya a karamar hukumar Dutsinma tare da Abubakar Saddi Bala dan shekaru 30 wanda aka samu da hannu dumu dumu a harkar satar mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Lawal Gurgu wanda shine ya tsara yadda aka sace wani attajiri mai suna Alh. Muntari Bala dake zama a unguwar Garo, garin Dutsinma, dubun sa ta cika yayin da ‘yan sanda sukayi masa dirar mikiya lokacin da yake waya da iyalan wanda aka sace domin neman kudin fansa har naira miliyan biyu,

Lawal Gurgu dai bai musanta laifinsa ba, a lokacin da yake bayani ga ‘yan sandan, inda ya bayyana cewa da farko sun nemi a biya kudin fansa har naira miliyan 20, aka gangaro zuwa miliyan goma inda daga karshe dai aka cimma matsaya kan naira miliyan biyu, tare da sharadin matukar ba a biya wannan kudi ba to zasu kashe attajirin da aka sace,

Yanzu haka dai rundunar ‘yan sandan ta jihar Katsina tana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan lamari.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0