Ina Fatan Samun Nasara A Kotu Kan Zaben Kano- Inji Abba Gida-Gida.

Ina Fatan Samun Nasara A Kotu Kan Zaben Kano- Inji Abba Gida-Gida.

Daga Mohammed Lawal :

Yayin da kotun kolin Nijeriya ta koma da ci gaba da sauraren shari’a kan kalubalantar nasarar da Abdullahi Ganduji ya samu a zaben gwamnan jihar Kano na ranar 9 ga watan Maris na 2019, dantakarar gwamnan a karkashin tutar PDP Abba Kabiru ya bukaci kotu ta bashi nasarar lashe zaben.

Abba Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, yace kasancewar shine ya samu kuri’u masu rinjaye, shine ya cancanci a  bashi nasarar lashe zaben tunda ya cika sharuddan sashe na  179 na dokar zabe.

Yace soke sakamakon zaben wasu kananan hukumomi da akayi wanda kuma ba bisa ka’ida ba ya bayar da damar yiwa PDP kwace.

Indai ba’a manta ba ranar 23 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar gwamna Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano.

To sai dai akwai sauran runa a kaba, kasancewa yanzu shari’ar na gaban kotun koli a ci gaba da kalubalantar nasarar gwamna Ganduje. Ranar litinin 13 ga wannan wata na Janairune aka sa ran kotun zata yanke hukunci, amma sabo da wasu dalilai kotun ta dage zamanta zuwa ranar 14 ga Janairu.

A zaman kotun na ranar 14 ga watan na Janairu, kotun ta tsaida ranar 20 ga Janairu domin yanke hukunci na karshe a kan zaben gwamnan na jihar Kano.

Mai shari’a Tanko Muhammad wanda ya jagoranci tawagar alkalan su bakwai shine ya sanar da dake sauraren shari’ar zuwa 20 ga wannan wata.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0