Najeriya Zata Sayo Littattafan ‘Yan Makarantar Firamare na Kudi har Biliyan 6.34.

Najeriya Zata Sayo Littattafan ‘Yan Makarantar Firamare na Kudi har Biliyan 6.34.

Daga Kabiru Yusuf, Abuja

Gwamnatin Najeriya zata sayo littattafan ‘yan Firamare musamman na ‘yan aji 1 zuwa 3 har na Naira Biliyan 6.34 a cewar Ministan Ilimin Kasar, Malam Adamu Adamu.

Malam Adamu Adamu wanda ya bayyana hakan ga manema labaran da ke Fadar mulkin Kasar, bayan kammala taron Ministocin da ake yi a mako-mako.

Haka kuma Ministan ya ce, zaman Majalisar ya amince da bada kwangilar ginin katangar da zata kewaye babban makwancin daliban jami’ar Maiduguri ta jihar Borno akan kudi Naira Biliyan 1.39

Ita ma ministar Kasa a ma’aikatar Kula da babban birnin tarayyar kasar, uwargida Ramatu Tijjani Aliyu, cewa ta yi, hukumar kula da birnin na Abuja, ta yi shirin gina gidaje dubu biyar masu sauki kudi. 

Inda ta kara da cewa, hukumar zata ware fili me fading kadada 30,000 a cikin kowace gunduma daga cikin gundumomi 6 na babban birnin.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 1