Najeriya Ta Sanar da Takaita Shigowar ‘yan Asalin Kashe 13 zuwa Kasarta Saboda Cutar Corona

Najeriya Ta Sanar da Takaita Shigowar ‘yan Asalin Kashe 13 zuwa Kasarta Saboda Cutar Corona

Mahmood Sadeeq Abuja

Gwamnatin Najeriya ta sanar datakaita shigar matafiya daga kasashe 13 da ake fama da  cutar Corona a duniya tare da haramta tafiye tafiye ga jami’anta zuwa wadanan kasashe, inda a yanzu aka samu Karin mutane biyar da suka kamu da cutar zuwa biyar a kasar tare, inda tuni ta dakatar  sanar da dage gudanar da bikin wasani na kasar

 Najeriya dai ta dauki wadannan sabbin matakai a kasar ne inda ta  bayyana kasashen 13 da suka hada da China, Jamus, Faransa da Italiya  da sauransu a matsayin kasashen da ta  takaita shoigar matafiya daga can zuwa kasar

Sakataren gwamnatin Najeriyar Boss Mustapha yace kasashen suna da mutane dubu daya ko fiye da haka na wadanda suyka kamu da cutar a kasarsu.

 ‘’Yace gwamnatin Najeriya tana takaitaa shigar matafiya daga wadanan kasashe sune China Italiya, Iran Koriya ta Kudu Spaniya Faransa Jamus da Amurikma da sauransu. Najeriyar ta dakatar da bada takardar bisa ga matafiya da suka iso kasar, wanda sabon tsari ne.

Alummar Najeriyar dai na kara matsawa a kan gwamnati ta sanar da rufe  kan iyakokinta kamar yadda wasu kasashe na Afrika suka yi saboda wannan cuta ta Corona.

Cutar Corona dai na kara durkusar da al’amurra a cikin Najeriya, inda a ranar Talata aka sanar da dakatar da bikin wasani na kasar.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0