Mutane dubu 22 suka bace a Arewa maso gabashi- inji ICRC.

Mutane dubu 22 suka bace a Arewa maso gabashi- inji ICRC.

Mahmood Sadeeq Abuja

Shugaban kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross, Peter Maurer yace  sama da mutane dubu 22 ne suka bace a yankin arewa maso gabashin Najeriya sakamakon rigingimun ta’adanci da aka kwashe shekaru goma ana fafatawa.

Yace wannan ne adadi mafi girma da kungiyar ta samu tattarawa a kasar sakamakon wannan lamari. Kungiyar ta ICRC tace kashi 60 cikin 100 na mutanen da suka bata yara kanana ne a lokacin da suka bace.

‘’Babban tashin hankalin iyaye shine rashin sanin inda ‘ya’yansu suke, yanayin da ke sanya cikin bakin ciki da hali na rashin tabbas’’ inji Maurer

Yace mutane na da ‘yancin sanin inda ‘ya’yansu suke kuma dole ne a dauki mataki na kawo karshen bacewar mutane.

A shekara ta 2018 hukumar tsara kasashen da ke fama da ta’adanci ta sanya Najeriya a matsayin kasa ta uku a jerin kasashen da suka fi fama da ta’adanci.

Shugaban kungiyar ta Red Cross ya zo Najeriya ne don bikin cikar kungiyar shekaru 70 da kafuwa inda ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kungiyoyin kare hakokin jama’a da ma iyayen da ‘ya’yansu suka bace.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0