Mun tabbata zamu samu galaba a shariar zaben shugaban kasa- Inji  PDP

Mun tabbata zamu samu galaba a shariar zaben shugaban kasa- Inji PDP

Mohammed Lawal

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta bayyana kwarin guiwarta cewa  dantakarar  ta a zaben shugabancin kasa zai  samu nasara a shariar zaben shugaban kasa dake gaban kotun daukaka karat a tarayya.

Kakakin jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan shine ya furta hakan jiya litinin, sai dai kakakin na jam’iyyar ta PDP yace Atiku zai samu nasarar nan ne idan kotun ta daukaka kara tayi adalci a sauraren shari’ar.

 Jam’iyyar PDP dai ta tsaya kai da fata cewa  dantakarar ta shine ya lashe zaben na shugaban kasa na shekara ta 2019, amma shugaban kasa da jam’iyyarsa ta APC idansu ya rufe wajen muzgunawa tare da yin kazafi ga Atiku Abubakar domin ganin an raba masa hankali a shari’ar da ke gabansu.

Da yake jawabi ga manema labaru, sakataren hudda da jama’a na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan yayi zargin cewa shugaba Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka a yakin neman zabensa a shekara ta 2015.

Yace rayuwar ‘yan Nijeriya a karkashin jagorancin PDP ta fi inganci idan aka kwatanta da   yanayin rayuwar ‘yan Nijeriya a karkashin jagorancin APC, don haka lokaci yayi da zamu sake karbe ragamar shugaban cin kasar.  

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0