Masu Zanga-Zanga  a Birnin – Gwari sun toshe hanya ga Gwamna El-Rufai

Masu Zanga-Zanga a Birnin – Gwari sun toshe hanya ga Gwamna El-Rufai

Daga Mahmood Sadeeq

Dubban matasa da ke zanga-zanga a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun toshe hanya ga gwamnan jihar Kaduna Nasiru EL-Rufa’I a lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga kauyen Kakangi inda ‘yan bindiga suka kai mumunan hari a yankin.

Gwamnan na jihar Kaduna yaje yankin ne domin ganewa idanunsa mumunan harin da ‘yan bindiga suka kai, inda suka rinka harbi tare da cinnawa gidaje da dama wuta. Bala’in ya yi dalilin mutuwar mutane da dama ciki har da ‘yan sanda biyu.

Matasan sun tilasatawa gwamnan ya sauka daga motarsa inda ya saurari koke-kokensu a kan hare-haren da ake kaiwa a yankin.

Karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna ta kasance cikin mumunan hali na hare-hare da ‘yan bindiga suke kaiwa alumma, abinda ya tilastawa mutane da dama yin kaura daga kauyukansu.

Sifeto Janar na ‘Yan Sanda Ya Kai Ziyara a Birnin –Gwari

Shima sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya sauka a garin Birnin-Gwari domin ganewa idanunsa halin rashin tsaro da ke adabar yankin.

Ya kai ziyarar ce  bayan da rundunar ‘yan sandan ta kadammar da wani shiri na musamman domin yakar masu satar mutane da kai hare-hare a yankin.

Karamar hukumar Birnin Gwari na fama da bala’I na masu kai hare- hare wadanda ke tsallakowa daga jihar Zamfara zuwa yankin. Manyan garuruwa na karamar hukumar watau na Randagi, Kuyello da Dogon-Dawa duka sun fukanci matsala ta sata da garkuwa da jama’a domin neman fansa, da hare-hare da ‘yan bindiga ke kawai. Wannan lamari ya haifar da mumunar koma baya ga harkokin kasuwanci da nomad a kiwo da alummar yankunan suka dogara da shi.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0