Kungiyoyin Yarabawa Sunyi Kira ga Buhari  da ya Haramta Amotekun.

Kungiyoyin Yarabawa Sunyi Kira ga Buhari da ya Haramta Amotekun.

Daga Mohammed Lawal :

Wata Kungiyar Yaraba ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar matakin sokewa tare da haramta kungiyar nan ta tsaro da aka kafa a yankin kudu maso yammacin Nijeriya da ake kira Amotekun, domin kaucewa zubar da jini a yankin.

Kungiyar  ta Yarabawa tace tun lokacin da aka kafa wannan Ametokun da sunan kungiyar tsaro domin inganta harkar tsaro a jihohin Yarabawa take ta cin zarafi tare da muzgunawa jama’a ba gaira ba dalili. Musamman ma a wannan hali na annobar Corona, kungiyar ta Amotekun tana amfani da wannan dama wajen tozarta jama’a, sabo da haka ana kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta soke wannan kungiyar tsaro ta Amotekun..

Kasancewar karancin jami’an tsaro a lokacin wannan annoba ta Covid-19, wasu membobin kungiyar suna amfani da wannan dama wajen zafafa kai hare haren kan fararen hula da sunan tabbatar da kiyaye dokar zaman gida domin dakile yaduwa annobar ta Corona.

Kungiyar ta Yarabawa tace Amotekun a halin yanzu tana nema maye gurbin ayyukan jami’an tsaro na yankin da karfin tuwo, don haka ya zama wajibi a dauki matakan gaugawa a kan kungiyar ta Amotekun domin kaucewa zubda jini.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0