Kungiyar Kwadao ta Nijeriya NLC Tayi Kira da a Rage Albashin ‘yan Siyasa,

Kungiyar Kwadao ta Nijeriya NLC Tayi Kira da a Rage Albashin ‘yan Siyasa,

Daga Mohammed Lawal  :

Biyo bayan wani yunkuri da hukumar Tarawa da rarraba kudaden shiga ta Nijeriya tayi kan sake fasalta albashin masu rike da mukaman siyasa a kasar,  Kungiya kwadago ta Nijeriya NLC tayi kira da a rage albashi da alawus na jami’an da abun ya shafa.

Shugaban kungiyar ta kwadago ta Nijeriya Ayuba Wabba shine yayi wannan kira a wani taron da yayi da ‘yan jarida a Abuja ranar talata, inda yayi nuni da cewa kudaden da ake biyan masu rike da irin wadannan mukaman siyasa a Nijeriya ya wuce kima.

Yace a duk duniya babu inda ake biyan masu rike da mukaman siyasa kamar a Nijeriya. Yayi nuni da cewa ma’aikatan da gwamnati da sauran al’ummar kasa kasuwa daya suke zuwa sayayya tare da irin wadannan ‘yan siyasa.

Wabba yace a tunani na sake fasalta albashi kamata yayi ayi kari maimakon a rage, amma ga masu rike da mukaman siyasa a Nijeriya, kama yayi a rage.

Shugaban kungiyar ta kwadago ya bayyana takaicinsa bisa ga yadda yayin da ma’aikatan gwamnati  ke karbar Naira dubu 18 a matsayin mafi karancin albashi, su kuma masu rike da mukaman siyasar hukumar ta kara masu albashi da kashi 800.

Wabba ya kara da yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar matakan da suka dace na shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar, inda yayi nuni da cewa ‘yan ta’adda na Boko Haram suna yawan kaiwa fararen hula hare hare a cikin ‘yan lokuttan nan.

Yayin da aka tambayeshi batun cecekucen da akeyi kan shugabannin sojojin kasar, Mr. Wabba cewa yayi baya so ya shiga cikin wannan siyasa dangane da ko a saukesu kokuma a barsu, wannan wani batu ne dake hannun shugaban kasa.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0