Kungiyar Addini ta Hakika mai halatta shan giya da zina ta bulla a Neja.

Kungiyar Addini ta Hakika mai halatta shan giya da zina ta bulla a Neja.

Mohammed Lawal

Gwamnatin jihar Neja ta haramta duk wasu ayyuka na kungiyar nan ta addini wadda ke halatta shan giya da zina a duk fadin jihar.

Wannan kungiya ta fara bulla ne a garin Mubi jihar Adamawa a ‘yan shekarun da suka gaba, mahukunta da malaman addini sun tashi tsaye wajen dakushe yaduwar wannan kungiya wadda take ta samun dinbin mabiya,musamman matasan da basu da aure kuma basu da aikin yi.

Babban daraktan kula da harkokin addini na jihar Neja, Dr. Umar farouk Abdullahi wanda ya sanar da matakin haramta kungiyar a duk fadin jihar ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnati ta dauki wannan mataki bisa ga la’akari da yadda kungiyar take ta habaka.

Jama’ar gari dai tuna suka fara yin korafi kan harkokin membobin wannan kungiya ta Hakika, wadanda suke ganin zasu gurbata wa jama’a tarbiya, musamman kasancewar ana cikin watan Ramadan, yayin da su kuma ‘yan wannan kungiya a wajensu azumin bai zama dole ba. Kasancewar a ko wane lokaci memba na kungiyar babu laifi ya kora ruwan barasa kokuma yayi lalata da mace.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0