Kudirin Kafa Dokar Boko Haram cin Fuskane- Inji Sanata Gyang.

Kudirin Kafa Dokar Boko Haram cin Fuskane- Inji Sanata Gyang.

Daga Mohammed Lawal :

Wani dan majalisar dattawan Nijeriya mai wakiltar jihar Plateau ta arewa, Sanata Istifanus Gyang yace yunkurin nan na samar da dokar da zata bada dama a kirkiro da hukumar kula da tubabbun ‘yan kungiyar Boko Haram, cin fuska ne ga ‘yan Nijeriya.

Jiya lahadi ne Sanata Gyang yayi wannan furucin a garin Jos, fadar gwamnatin jihar Plateau, inda yayi nuni da cewa shirin dokar zai samar da nakasu ga tsaron kasar nan, don haka yayi kira ga sauran takwarorinsa sanatoci da suyi watsi da wannan kudiri.

Yace shirin dokar zai kasance tamkar fami ga ciwon da dubban al’ummomi ke fama dashi, wato wadanda suka sha akuba daga hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram. Kasancewa har yanzu basu manta ba da irin yadda ‘yan kungiyar ta boko haram ta karkashe masu ‘yan uwa  ta yiwa matansu fyade ta kone masu gidajensu.

 Ranar alhamis din makon jiya ne Sanata Ibrahim Gaidam, mai wakiltar gundumar yammacin jihar Yobe ya gabatar da kudurin kafa wata hukuma wadda zata rinka kulawa da membobin kungiyar Boko Haram da suka tuba, da nufin daidaita masu tunani tare da tallafa masu da abin yi ta yadda zasu iya rayuwa cikin al’umma kamar kowa.

 Rahotanni daga mahukunta soja Nijeriya sun nuna cewa yanzu haka akwai zaratan Boko Haram wadanda suka tuba da yawansu zai kai 608 wadanda ake baiwa horo domin sauya masu tunani a kuma rabasu da wannan mummunar akida.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0