Ku Barmu Mu Sanya Hijabinmu Wadanda Suke So Su Tafi Tsirara……Inji Mata Musulmai

Ku Barmu Mu Sanya Hijabinmu Wadanda Suke So Su Tafi Tsirara……Inji Mata Musulmai

Mahmood Sadeeq

Wasu kungiyoyin musulmai a karkashin gamaiyyar kungiyoyin musulmai ta Najeriya sun yi kira ga gwamnmati a dukkanin matakai su ja kunen malaman da ke wuce iyaka, da ma jami’an gwamnati da su daina hana matan musulmai sanya hijabi.

Sun bayyana cewa sanya hijabi ‘yanci ne da tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya baiwa Najeriya don haka ba wanda ke da ikon hanawa musulmai sanya hijabi.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a birnin Lagos wajen bikin ranar sanya hijjabi ta duniya, inda suka yi zanga-zangar lumana a kan lamarin.

Daraktar kungiyar jadada ikon sanya hijabi ga mata Musulmai Mutiat Balogun tace mutanen da yawa basu san cewa matan da ke sanya hijabi na fuskantar muzgunawa da cin zarafinsu ba, duk kuwa da cewa wannan ‘yancinsu ne.

A duk lokacin da macen da ke sanye da hijabi taje neman lasisin tuka mota, ko pasgo na kasa da ma katin zama dan kasa, ana tursasa mata sai ta cire hijabi kafin a yi mata hoto.

‘’A sani tsarin mulki ya kare mana wannan ‘yanci na mu sanya  hijabi, a sani ba sai mun cire hijabi ba, don haka muka fito don wayar da kana jama’a su san cewa wannan ‘yancinmu ne’’

Takadamma A Kan Sanya Hijabi

Mata mususlmai a Najeriya sun dade suna fuskantar muzgunawa a kan sanya hijabi, musamman wadanda ke aikin gwamnati, dalibai a makarantun firamare, sakandire da ma jami’a da saunransu.

A shekarar 2017 ne wannan batu ya sake tasowa lokacin da makarantar yaye lauyoyi ta hana wata daliba musulma Firdausi Amusa shiga jerin daliban da za’a yaye saboda ta ki cire hijabinta.

Lamarin ya haifar da cece-kuce, amma dagewar da mususlmai suka yi ya sanya makarantar sauya wannan mumunar doka.

Mai martaba Sultan na Sokoto kuma Sarkin Musulman Najeriya Sa’ad Abubakar yace abinda ba’a sani ba shine sanya hijabi kare mutunci ne ga ‘ya mace musulma.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0