Kotun ta Yanke wa Maryam Sanda Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya.

Kotun ta Yanke wa Maryam Sanda Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya.

Daga Kabiru Yusuf, Abuja 

Babbar kotun shari’a a Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya. 

Mai shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun sharia’a dake Abuja ne ya zartar da hukuncin kisan ga wadda ake zargi, Maryam Sanda da kashe mijin nata Bilyaminu Halliru.

Kamar yadda mai shar’ar ya bayyana, Maryam Sandan zata fuskanci kisan ne ta hangar ratayewa. Inda Alkalin ya ce an yanke hukuncin ne kamar yadda binciken ‘yan Sanda ya tabbatar.


Alkalin ya ce, hukuncin nasa ya biyo bayan kasa kare kanta da Maryam din ta yi kan zargin kisan da ake yi mata na kashe marigayi Bilyaminu Halliru a daren Nuwamban shekarar 2017.

“Ke Maryam Sanda, Kotu ta same ki da laifin kashe mijinki, Bilyaminu Halliru. Domin haka kotu ta yake miki hukuncin dai-dai da laifin da ki ka aikata. Domin wannan ba wai abin takaici ba ne kawai, illa keta,” inji mai Shari’a.

Da jin haka Sai Maryam ta barke da kuka tana cewa: “Inna Llillahi wa inna illaihi Raji’un”.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0