Kotu ta yi fatali  da karar Atiku ta tabbatar wa Buhari da nasara.

Kotu ta yi fatali da karar Atiku ta tabbatar wa Buhari da nasara.

Mahmood Sadeeq Abuja :

Kotun sauraren  kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da karara da dan takarar neman shugtaban kasa na jamiyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar a gabanta inda ya kalubalanci nasarar da shugaban Najeriya ya samu.

An dai kwashe sao’i 9 ana wannan shari’ar kafin kammala yanke hukunci a kanta.

Shugaban kwamitin alkalan da suka yanke shari’ar, alkali Mohammed Garba ya yi watsi da karar da Atiku Abubakar ya shigar , ya bayyana hakan ne bayan yanke hukunci daya bayan daya a kan batutuwan da aka gabatar.

Kotun ta tabbatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci ya tsaya takara a zaben da aka yi, sai dai ta yi watsi da batun cewa Alhaji Atiku Abubakar na jamiyyar PDP ba dan Najeriya bane.

Bakin alkalan guda biyar dai ya zo daya, inda suka amince da watsi da wannan kara.

Amma  lauyoyin Atiku Abubakar sunce zasu garzaya kotun daukaka kara, domin kalubalantar wannan hukunci da alkalan suka yanke.

Shi kuwa shugaban Jam’iyyar ta APC na kasa Adam Oshiomole cewa yayi su kam basu da wani fargabar cewa sune zasu sama galaba a kan wannan shari’a.  

‘Ya’yan jamiyyar ta APC mai mulki na can suna murna da sakamakon shari’ar da suka ce ya nuna tabbacin gaskiya da sahihancin zaben.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0