Kotu ta bada belin Zakzaky da matarsda don suje neman magani a kasasr waje

Kotu ta bada belin Zakzaky da matarsda don suje neman magani a kasasr waje

Daga Edita

Wata kotu a Kaduna Najeriya ta bda belin  shugaban yan Shi’a na Najeriya Sheik Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenatu don su je a duba lafiyarsu a kasar Indiya.

Kotun ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta saki Sheikh Zakzaky da matarsa bisa beli domin a duba lafiyarsu.

Alkalin babban kotun da ke Kaduna mai shari’a Darius Khobo ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta saki Sheikh Zakzaky da matarsa domin su je a duba lafiyarsu a kasar India.

Tun da farko dai lauyan da ke kare Sheikh Zakzaky Femi Falana ne ya gabatar da wata sabuwar bukata a kan batun. Mr Falana yace akwai rahotani da suka kai takwas daga likitocin Najeriya da na kasashen waje da suka amince cewa Zakzaky na bukatar a duba lafiyarsa, kuma ba inda za’a iya yi mashi magani a cikin Najeriya.

Tun a watan Disambar 2015 azke tsare da shi abinda ya haifara da mumunan zanga-zanga a Abuja da sauran biranen Najeriya da ma a birnin London.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0