Kirkirowa Sanusi Sabuwar Masarauta a Kaduna- APC Kano ta Fadawa El-rufa’i.

Kirkirowa Sanusi Sabuwar Masarauta a Kaduna- APC Kano ta Fadawa El-rufa’i.

Daga Mohammed Lawal :

Jiya Litinin ne Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta maida martani bisa ga mukaman da gwaman Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya baiwa tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi.

Jam’iyyar ta APC reshen jihar Kano ta yi kira ga El-Rufa’I da ya kirkiro wata sabuwar masarauta a jihar ta Kaduna ga tubebben basaraken na Kano, Muhammadu Sanusi na 2.

A makon da ya gabata ne gwamna El-Rufai ya baiwa tsohon basaraken mukamin mataimakin shugaban hukumar kula da bunkasa saka jari ta jihar Kaduna (KADIP), ‘yan sa’o’I kadan da tsige tsohon sarkin. Sannan kuma daga bisani gwamnan ya bashi mukamin shugaban jami’ar jihar Kaduna.

Gwamnan ya kara nuna goyon baya ga tsohon sarki Sanusi yayin da ya kai masa ziyarar goyon baya a garin Awe na jihar Nasarawa, inda aka tura tsohon sarkin gudun hijira.

 A cikin jawabi mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC a jihar Kano, Alh. Shehu Maigari, jam’iyyar ta APC ta bukaci gwamna Nasiru El-Rufa’I da ya kirkiro da wata sabuwar masarauta a jihar Kaduna, domin ya baiwa Sanusi Lamido sarauta.

Yace “Haba gwamna Nasir el-Rufai, wannan mutun babu irin zagon kasa da bai yiwa wannan jam’iyya ta APC ba, wadda kuma itace jam’iyyar da kake tunkaho da ita, sannan kuma ya fito fili yana suka ga shugaban mu Muhammadu Buhari, ba tare da hujja ba, amma ya ka fito kana kambama shi tamkar wani gwarzo”.  

“Mai girma gwamna, jam’iyyar APC reshen jihar Kano tana rokon ka da ka kirkiro da wata sabuwar masarauta a jihar ka, watakila daga Rigachikun zuwa Kasuwar Magani, domin ka nada gwarzon naka a matsayin sarki, ta yadda zai ji dadin yiwa jam’iyyarsa ta PDP aiki yadda ya kamata, maimakon ka buge da yiwa masa wadannan nade naden mukamai na jeka na yika.  

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0