Kar ka Sake Komawa Borno- Shekau ya fadawa Buhari.

Kar ka Sake Komawa Borno- Shekau ya fadawa Buhari.

Daga Mohammed Lawal :

Shugaban kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram, Abubakar Shekau ya aika da sakon gargadi ga shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, inda a cikin sakon yake gargadinsa da kada ya kuskura ya sake komawa Borno.

A cikin wani faifan bidiyo da kamfanin sadarwa na The Cable ya samu, shugaban na kungiyar Boko Haram ya fito karara ya shaidawa Buhari cewa membobin kungiyar Boko Haram suna nan daram a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Don haka yace matukar shugaban Buhari ya sake saka kafarsa a jihar ta Borno, to babu abinda zai hana su kai mashi hari. Sabo da haka a cewar Shekau, in kunne yaji jiki ya tsira.

Shekau ya kuma kara da gindaya sharudda na sako ‘yammatan Chibok da kungiyar ta sace take garkuwa dasu tun 15 ga watan Aprilun 2014.

Daga cikin sharuddan akwai na sako membobin kungiyar ta Boko Haram wadanda yanzu haka ake tsare dasu.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0