Kano na ci Gaba da Kulle kan Iyakokinta ga Baki.

Kano na ci Gaba da Kulle kan Iyakokinta ga Baki.

Daga Mohammed Lawal :

A ci gaba da garkame kan iyakokinta ga baki masu son shiga jihar, a matsayin matakin dakile yaduwar cutar Corona, hukumar sa ido kan zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano ta kame motoci masu tarin yawa wadanda sukayi kokarin shiga jihar ta Kano daga wasu jihohin kasar, musamman daga yankin kudanci inda ake samun bullar wannan cuta ta Corona.

Kakakin hukumar dake sa ido kan zirga zirgar ababen hawan ta jihar Kano, wato hukumar da aka fi sani da KAROTA, Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, yace an kame wadannan motoci da suka yi yunkurin shiga Kano a wurare daban daban.

Ya kuma kara da cewa hukumar ta KAROTA ta gano wasu barayin hanyoyin da masu ababen hawan suke satar hanya suna shiga jihar daga wasu jihohi.

Malam Abubakar Kofar Na’isa yace akwai kimanin fasinjoji 350 da suka fito daga jihohin dake makwabtaka da jihar ta Kano wadanda aka tilastawa komawa inda suka fito.

Don haka ya shawarci matafiya dake da bukatar da zuwa jihar Kano da su jingine aniyar tasu har zuwa lokacin da gwamnati ta janye wannan haramci na shiga jihar ta Kano, musamman manyan motocin safa safa dake tasowa daga kudancin kasar zuwa jihar Kano.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0