Jihar Bauchi ta Karbi Daruruwan Almajirai daga wasu Jihohi.

Jihar Bauchi ta Karbi Daruruwan Almajirai daga wasu Jihohi.

Daga Mohammed Lawal :

Kamar sauran jihohin arewacin Nijeriya, itama  jihar Bauchi ta karbi kimanin almajirai  214 tare da malamai 8 ‘yan asalin jihar da aka maido mata daga jihar Plateau a ranar Lahadi, inda mataimakin gwamnan jihar ta Bauchi Alh. Baba Tela ya karbi wadannan almajirai da malamansu a harabar kwalejin tunawa da janar Hassan Usman Katsina dake Bauchi.

Yayin da aka iso da wadannan almajirai an tantancesu, sannan kuma aka basu sinadarin kashe kwayoyin cuta suka shafawa hannuwansu, daga bisani aka kaisu masauki a dakunan kwanan dalibai na kwalejin suka yi wanka suka ci abinci.

Jami’in kiwon lafiya na jihar ya bayyana cewa washe gari an auna yanayin zafin jikin ko wane almajiri daga cikinsu  domin tabbatar da lafiyarsu kafin a turasu zuwa garuruwansu.

Akwai kuma wasu karin almajiran da ake sa ran maidosu a jihar ta Bauchi daga jihohin Kano da Gombe, yayin da itama jihar Nasarawa zata izo keyar almajirai 700 ‘yan asalin jihar ta Bauchi tare da malamansu.

Gwamnatin jihar ta umurci shugabannin kananan hukumomin jihar da su tabbatar da sun maida wadannan almajirai dake karkashin kananan hukumominsu zuwa kauyukansu, idan ba haka ba kuma duk almajirin da aka samu yana ragayta za’a tuhumi shugaban karamar hukumarsa da laifin yin sakaci.

Wannan mataki yana daya daga cikin matakan da gwamnonin arewacin Nijeriya suka cimma matsaya akai na kawar da almajirci kwata kwata musamman a wannan lokaci na yaki da annobar Covid-19.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0