Jakadan Kasar Saudiya A Najeriya Adnan ya Rasu A Abuja

Jakadan Kasar Saudiya A Najeriya Adnan ya Rasu A Abuja

Daga Kabiru Yusuf Abuja

Allah ya yi wa Jakadan Kasar Saudi Arabia a Najeriya, Adnan Mahmoud Bostaji rasuwa. Ofishin jakadancin Kasar Saudiyar ne ya tabbatar da haka a yau Talata.

Ambasada Adnan ya dawo daga kasar Saudiyya a ranar Litini cikin koshin lafiya, amma kuma da safiyar Talata rai ya yi halinsa.

An fara sanar da rasuwar ne ta kafar sada zumunta ta Facebook kafin ofishin ta bada tabbacin hakan.

Bayanai sun ce da safiyar Talata ne aka shiga dakinsa domin ba’a ji motsin tashinsa ba, sai kawai aka iske daga barci ya rasu.

Dama dai wa’adin aikinsa a Najeriya ya cika sauran ‘yan makwani suka rage masa, don haka ne ma ya tura iyalansa gaba daya zuwa Saudiyya.

Sanarwar ta ce ” Muna Masu sanar  da ku cewa, Allah ya karbi ran bawansa, Jakadan Kasar Saudiya dake Najeriya, Shiekh Adnan Mahmoud Bostaji.”

Rasuwar Jakadan dai ta kada mutane da dama ainun, musamman yadda abin ya zo faf daya, duk da sabawa a kullum mutuwa bakuwa ce gab ani Adama.

Bayanai sun ce za’a dauki gawarsa zuwa kasar Saudiyya domin yi masa janaiza kafin a birne shi a can.

Da fatan Allah ya jikansa da rahama Ameen.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0