In ba Ayi Hankali ba, Najeriya zata sake fadawa cikin matsalar tattalin arziki- Inji -CBN

In ba Ayi Hankali ba, Najeriya zata sake fadawa cikin matsalar tattalin arziki- Inji -CBN

Kabiru Yusuf

Gwamnan babban bankin Najeriy, CBN, Godwin Emefiele, ya ce yana tsoron kada Najeriya ta sake fadawa cikin matsalar tattalin arziki ganin yadda al’amura ke tafiya a yanzu.

Ya ce ya zama wajibi a dauki matakai domin a dakatar da yadda rashin matsalar aikin yi a kasa da sauran matsalolin da tattalin arziki ke fuskant, in har ana son kaucewa sake fadawa cikin wannan matsala.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Jami’ar jihar Benin a yayin da yake gabatar da wata lacca mai taken “Kaucewar Duniya daga  shiga matsin tattalin arziki: Tsaron hada-hadar kudade ta Duniya domin kaucewa rashin tabbas”.

Kamar yadda ya bayyana, Emefiele ya kara da cewa dole ne sai Hukumar hada-Hadar kudaden da tare tsare ta tashi tsaye wajen fuskantar matsalolin da suka fara kunno kai domin ayi maganinsu.

Gwamnan ya ce ” In an lura kawai alamun rashin tabbas yanzu a Duniya wanda ke nuni da cewa a matsaloli dake kunno kai, wadanda ke nuna alamun kawai matsalar a nan gaba.

“Abin tambaya a nan shine, wace hanya mahukuntan da ke kula da harkokin hadahadar kudaden Najeriya ke shirin bi wajen kaucewa sake fadawa cikin wannan matsalar?.

” Ganin a baya mun shiga irinta amman muka samu nasarar fitar daga ita. Za mu iya tunawa da halin da hauhawar farashin kaya ta jefa mu a ciki a can baya wanda ya dakatar da bunkasar tattalin arzikin Kasar mu da kashi 18.72 cikin dari a shekarar 2017, amma a yanzu ya komo 11.37. Mun ga yadda lalitar ajiyarmu ta Kasashen wajen ta samu tagomashi, canjin kudaden kasar waje ya tsaya wajen guda, amma abin takaici shine harbyanzu nuna fuskantar barazana daga yawan matasan sa basu da aikin yi”. Inji Gwamnan.

Saboda haka sai gwamnan ya ba da tabbacin cewa babban bankin Kasa zai ci gaba da daukar matakai wajen ganin Najeriya ta kaucewa kunnowar wasu sabbin matsaloli daga kasashen duniya

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0