Hukumar Custom ta Cafke Dala Miliyan 8 a Filin Jiragen Saman Lagos

Hukumar Custom ta Cafke Dala Miliyan 8 a Filin Jiragen Saman Lagos

Daga Kabiru Yusuf, AbujaH

Hukumar Hana Fasa Kauri ta Najeriya, wato Custom ta kama sama da Dala miliyan 8 a filin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Lagos.

Gidan Radiyon Faransa ya wallafa a shafinsa cewa, Shugaban Kwastam, Hamid Ali ya bayyana wa manema labarai cewa, an cafke makudea kudaden ne a cikin wata mota a daidai lokacin da ake shirin loda su cikin jirgin sama.

Sai dai Hamid bai bada cikakken bayani ba kan jirgin da aka yi nufin dakon kudin da shi, amma a cewarsa, motar da aka zuba kudina ciki, mallakar Hukumar Kula da Kayayyakin Jiragen Sama ta Najeriya (NAHCO) ce.

Wani shaidar gani da ido da ya bukaci mu sakaya sunansa, ya ce, duk wani babban jami’in tsaro a filin jirgin saman na kasa da kasa, na da masaniya kan wannan makarkashiya.

Tuni aka cafke direban motar da kuma wani ma’aikacin Hukumar ta NAHCO saboda zargin su da hannu a yunkurin wawure dukiyar kasa.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0