Gwamnati ta Kara Rage Farashin Man Fetur, ta Kuma Dakatar da Karin Farashin Lantarki.

Gwamnati ta Kara Rage Farashin Man Fetur, ta Kuma Dakatar da Karin Farashin Lantarki.

Daga Mohammed Lawal :

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kara rage farashin Man fetur daga Naira 125 wanda ta sanar ‘yan kwanakin baya zuwa Naira 123 da kwabo 50. Sannan kuma a waje daya hukumar sanya ido kan wutar lantarki ta jingine batun nan na karin farashin wutar lantarki wanda tayi niyyar fara aiwatarwa daga wannan wata na Aprilun 2020.

Jiya talata ne da dare, sakaren gudanarwa na hukumar kayyade farashin albarkatun man fetur, Mr. Abdulkadir Sa’idu ya sanar da hakan a Abuja, inda ya kara da cewa daga ranar 1 ga wannan wata na Aprilu ne wannan sabon farashin zai fara aiki.

Kazalika shima ministan wutar lantarki na Nijeriya, Injiniya Saleh Mamman wanda ya sanar da dakatar da karin farashin wutar lantarkin cewa yayi an dauki wannan matakine da nufin saukaka rayuwa ga ‘yan Nijeriya, musamman a wannan yanayi na annobar Coronavirus.

Ministan ya kara da yabawa kamfanonin rarraba wutar lantarkin  bisa ga alkawarin da suka dauka na tabbatar da suna samar da wutar lantarkin ga jama’a yayin da aka shiga wannan mawuyacin hali, ya kuma roke su da su cika alkawarin da suka daukarwa ‘yan Nijeriya.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0