Gwamnan Jihar Bauchi Ya Kamu Da Cutar Corona

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Kamu Da Cutar Corona

Mahmood Sadeeq

Gwajin da aka yiwa Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya nuna cewa gwamnan na dauke da kwayar cutar Corona da ake yiwa lakabi da Covid 19

Gwamnan ya sanar da shawarar da ya dauka ta kebe kansa saboda wannan matsala.

Gwamna Bala Mohammed yace ya hau jirgin sama tare da Mohammed wanda Da ne ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar.

A sanarwar da kakakin gwamnan na jihar Bauchi  Muktar Gidado ya sanya hannu ta bayyana cewa gwaji ta nuna gwannan na da kwayar cutar a jikinsa, daga cikin mutane shida da aka yiwa gwajin.

Cutar da Corona dai na ci gaba da yaduwa a Najeriya musamman a biranen Lagos da Abuja hedikwatar Najeriya.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0