Guguwa mai karfi ta yi mummunar barna a Abuja

Guguwa mai karfi ta yi mummunar barna a Abuja

Wata iska mai karfin gaske da tashi a daren asabar dinan ta yi mumunar barna a unguwar Galadimawa da ke Abuja. Iskar da ta kada kusan tsakiyar dare ta tikastawa jama’a farajawa daga barci afirgice.

Wani mazaunin unguwar Galadamiawa Greg Anor ya shidawa Hantsi  cewa, karar iskar day a ji da yadda take kwashe tarkacen da ta ci karo da so sun sanya dole ya tashi daga barci. Greg yace barci da bai sake yi ba kenan domin da yawan makwabtansa iskar ta kware kwanon rufn dakunanasu.

‘’In tsakiyar barci naji karar guguwar tana daga kwanon gida da awon gaba da takarci, ba arziki dole na tashi firgigi’’. Inji Greg Anor

Yace kodayake shi bai yi asara ba, amma akwai mutane da dama da suka rasa kayayyakinsu, wasu kuwa shagunan da suke sana’a ta yi fatafata da su.

Wazi mazaunin unguwar Abubakar Tanko  yace ya kasa zuwa koina domin iskar ta lalata gaba dayan ‘yan kayansa.

Mazauna unguwar ta Galadimawa na kira ga gwamnati ta kai masu dauki bisa wannan bala’i.

Yanayin zafi ya cnaza a Abuja

A bana dai an samu sauyin yanayi sosai a Abuja, inda a wasu lokutan yanayin zafin yakan kai har maki 42 bisa maunin zafi a babban birnin na Najeriya.

Masana sauyin yanayi da muhalli sun ce wannan sauyi na nuna tabbata ta sauyin yanayi a yawan zafin da duniya ke yi, inda sannu a hankali ake fukantar tsananin sanyi da zafi a kasar nan. Kodayake akan samu iska a farkon damuna a Abuja, amma ba kasafai take irin wannan barna ba.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0