Ganduje Ya Tsige Sanusi Daga Karagar Mulkin Kano.

Ganduje Ya Tsige Sanusi Daga Karagar Mulkin Kano.

Daga Mohammed Lawal :

A yau Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da tsige sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga karagar mulki bisa ga aikata laifin raini ga ofishin gwamna da sauran hukumomin  gwamnatin jihar.

A cikin takardar sanarwar da aka rabawa manema labaru mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Alh. Usman Alhaji, ya bayyana cewa gwamna Ganduje ya amince da tsige Sanusi Lamido daga karagar mulki ba tare da bata lokaci ba.

Yace Sarkin na Kano yana nuna raini ga ofishin gwamnan jihar Kano da sauran hukumomin gwamnatin jihar, daga cikin irin wannan halayya ta raini akwai kin halartar taruka da sauran shirye shiryen da gwamnatin ke shiryawa ba tare bada gamsasshen uzuri kauracewa irin wadannan taruka ba, abinda ake gani a matsayin taurin kai.

Yace kara da cewa sanin kowane Sanusi Lamido an same shi da laifin yin karan tsaye ga sashe na 3, sakin layi na 13 na dokar masarautar Kano ta 2019, don haka muddin ba’a dauki matakin da ya dace ba martabar masarautar zata zube.

Yace an dauki matakin tsige sarkin ne biyo bayan tuntubar da aka yiwa masu ruwa da tsaki a masarautar, abinda kuma ya zo daidai da tanadin dake kunshe a sashe na 3 na dokar masarautar ta 2019, gami da sauran kwararan dalilai.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun, sannan kuma su kiyaye doka da oda..

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0