Elrufai ya bullo da hutun watanni 6 ga matan da suka haihu

Elrufai ya bullo da hutun watanni 6 ga matan da suka haihu

Daga Mahmoud Sadeeq

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru Elrufa’i ya sanar da sabon tsarin hutu na watanni shida ga Matan da suka haihu.

A jawabinsa na rantsuwar kama aiki a zango na biyu, gwamnan yace, an bullo da tsarin ne son baiwa mata ikon murmurewa daga haihuwa.

A bisa wannan tsari da ya yi dai dai da na wasu kasashen turai, zai baiwa mata masu jego da ke aikin gwamnati damar kula da jariransu sosai.

Gwamnan yace kula da lafiyar al’umma abu ne mai muhimmanci gaske ga gwamnatin ta jihar Kaduna.

Matan da suke aikin gwamnati kuma suke shayarwa kan fuskanci kalubale mai yawa.

Kwararru na yaba tsarin hutun a matsayin wanda zai bada damar baiwa jariri nonon uwa na watani shida ba tare da basu ruwa ba.

Tsarin da hukumar lafiya ta duniya ta dade da bada shawarar aiwatar da shi.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0