El-Rufai ya Baiwa Sanusi Lamido Mukami a Hukumar Saka Jari ta Kaduna.

El-Rufai ya Baiwa Sanusi Lamido Mukami a Hukumar Saka Jari ta Kaduna.

Daga Mohammed Lawal :

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’I ya nada tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a matsayin mataikin shugaban hukumar kula da zuba jari ta jihar Kaduna (KADIPA)kwana daya bayan tsige shi daga mukamin sarkin Kano da gwamna Abdullahi Ganduje yayi.

Ranar litinin ce aka sanar da tsige tsohon basaraken, sannan kuma aka iza keyarsa zuwa zuwa gudun jihira a jihar Nasarawa, inda kuma ake tsare da shi bisa ga umurnin Ganduje.

Jiya talata ne Mr. Muyiwa Adekeye, mai baiwa gwamna El-Rufai shawara kan kafofin yada labarai ya sanar da nadin, inda ya kara da cewa wannan wani bangarene na sake fasalta majalisar hukumar ta zuba jari, wadda ke karkashin shugabancin mataikiyar gwamnan jihar, wadda kuma ta kunshi manyan jami’an gwamnatin jihar a matsayin membobi.

Yace “Jihar Kaduna tana fatar ganin ta amfana daga dinbin basirar Sanusi Lamido Sanusi, wanda kafin ya zama sarki yayi fice a duniya ta fannin harkar kudade.

Ya kuma kara da cewa abin alfari ne ga jihar Kaduna ta amfana daga dinbin basirar wannan fitaccen mutun, wanda yayi suna a duniya domin ciyar da jihar gaba.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0