DSS ta yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da kiran juyin-juya hali.

DSS ta yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da kiran juyin-juya hali.

Mahmood Sadeeq

Hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da barazanar gudanar da juyin juya hali da Mr Omoyele Sowore ya yi a kasar.

Mr Sowore wanda shine mai buga jaridar nan ta Sahara Reporters wanda tuni hukumar ta DSS ta cafke shi, ya shirya gudanar da zanga-zangar ce a ranar litinin din nan 5 ga watan Augusta.

Jami’in yada labaru na hukumar ta DSS Mr Peter Afunanya shine ya yi kiranm a lokacin da ya gana da manema labaru a Abuja.

Yace an kame Sowere ne saboda barazanar da yake ga yanayin zaman lafiya da walwalar jama’a.

Hukumar tana da nauyin kare yanayin tsaro, lafiya da walwalar jama’a a kasar nan.

‘’Idan har muna aiki a matsayinmu na hukumar tsaro da tasan abinda take yi, sannan wani na kiran a yi juyin juya hali a Najeriya ai dole ne m,u fahimci shin me yake nufi da haka’’

Yace abinda wannan ke nufi shine sunkuru, tana nufin karbe gwamnati da karfi, kuma ai an san muna a mulki ne na dimukurdiyya.

Kakakin hukumar ta DSS yace hukumarsa da sauran hukumomin tsaro zasu yi duk abinda zasu iya domin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0