Cutar Corona Virus ta Kashe Mutane 80, Yayinda wasu 3000 na Asibiti.

Cutar Corona Virus ta Kashe Mutane 80, Yayinda wasu 3000 na Asibiti.

Daga Kabiru Yusuf, Abuja

Mahukuntan kasar China sun bayyana cewa ya zuwa yammacin jiya lahadi, cutar ‘Corona Virus’ ta halaka mutane 80 yayin da wasu 3,000 ke kwance a Asibiti.

Kididdigar da mahukuntan Kasar ta China suka fitar, ta ce, baya ga mutane 80 da suka riga mu Gidan gaskiya, akwai mutane 2,744 da suka kamu da cutar yayin da ake zargin mutane 5,794 da kamuwa da kwayoyin cutar,46 kuna Suna cikin halin mutu-kwakwai – rai kwakwai yayin da aka sallami mutane 51 bayan sun samu sauki.

A dazu ne Firemiyan kasar ta China, Li Keqiang ya kai ziyara garin Wuhan inda wanna cuta ta fara bulla.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 1