Cutar Corona Ta Sa An Dakatar Da Shirin  Sanin Makama na Masu Yiwa Kasa

Cutar Corona Ta Sa An Dakatar Da Shirin Sanin Makama na Masu Yiwa Kasa

Mahmood Sadeeq

Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta NYSC ta sanar da dakatar da shirin makaman aiki  na masu yiwa kasa hidima a Najeriya.

Babban Daraktan hukumar Birgadiya Janar Shuaibu Ibrahim ne ya sanar da haka, yace an dauki matakin ne a matsayin na kariya saboda barkewar cutar Corona a Najeriya.

Da safiyar Larbar nan aka umurci dukkanin masu yiwa kasa hidimar da su watse  daga sansani9n sanin makmar aiki da ke jihohin Najeriya, su tafi  gidajensu.

Babban daraklta yace kodayake ba’a samu  bullar cutar a tsakanin masan ba, amma sun dauki matakin ne don akucewa afkuwar hakan.

A bisa jadawalin  shirin sai ranar 30 ga watan Maris dinan ne ya kamata su bar sansanin.

Koda a lokacin da aka samu bullar cutar Ebola ma irin wannan mataki aka dauka, domin kaucewa cunkoson jama’a da yiwuwar kamuwa da cutar.

Najeriya dai na fusknatar kalubale inda aka samu Karin yawan mutanen da ke dauke da cutar a kasar.

Gwamnati dai tace a kwantar da hankali a kan wannan lamari.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0