Covid19 : Za’a Rufe Makarantu a Arewacin Nijeriya ; Lagos ta Haramta tarukan Addini.

Covid19 : Za’a Rufe Makarantu a Arewacin Nijeriya ; Lagos ta Haramta tarukan Addini.

Daga Mohammed Lawal :

Gwamnoni yankin arewa maso yammci da na yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya sun cimma matsaya kan daukar matakan dakile yaduwar muguwar cutar nan ta Corona zuwa yankin.

Gwamnonin sun yanke shawarar rufe makarantun boko na duk fadin yankin har na tsawon kwanaki 30 daga ranar Litinin 23 ga wannan wata na Maris.sabo da fargabar yaduwar cutar Coronavirus.

Wannan shawara tana kunshe ne a cikin takardar bayan taro na majalisar gwamnonin yankin arewa maso yammacin Nijeriya wadda ke dauke da sa hannun shugaban taron, Alh. Aminu Bello Masari da takwaransa na jihar Niger, Sani Bello da aka gudanar a garin Kaduna jiya Laraba.

Baya ga wannan kuma, taron gwamnonin sun amince su tara kudi domin samar da tsaro da nufin magance ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

 Gwamnonin sun yanke shawarar tuntubar hukumomin shirya jarabawa ga makarantun sakandare kafin su rufe makarantun a ranar 23 ga watan Maris da muke ciki..

 A waje daya kuma,jiya laraba ne gwamnatin jihar Lagos ta haramta duk wasu taruka na addini da zai kunshi akalla mutane 50 a duk fadin jihar, har na tsawon makonni hudu masu zuwa.

 Kwamishinan kula da harkokin cikin gida na jihar Legas,Prince Olanrewaju Elegushi wanda ya sanar da hakan ga manema labaru a Ikeja, jim kadan bayan wata ganawar sirri da shugabannin addini na jihar dangane da yadda za’a bullowa yaki da wannan cuta ta Coronavirus, yace haramcin kan tarukan addini ya fara aiki nan take.

Yace an yanke wannan shawara ne domin kare al’ummar jihar Legas daga wannan annoba ta Coronavirus.

Yace “Mun gana da shugabannin musulmai da na kiristoci, mun kuma tafka muhawara, inda daga bisani muka cimma matsaya cewa kare rayukan al’ummar jihar Legas shine babban abu mafi mahimmanci”.   

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0