Covid-19 : Gwamnati ta Daukewa ‘Yan Nijeriya Biyan Kudin Wuta na Wata 2.

Covid-19 : Gwamnati ta Daukewa ‘Yan Nijeriya Biyan Kudin Wuta na Wata 2.

Daga Mohammed Lawal  :

Kamfunnan  rarraba wutar lantarki a fadin Nijeriya (DisCos) sun ce zasu hada guiwa da gwamnatin tarayya wajen samar da wutar lantarki kyauta ga ‘yan Nijeriya har na tsawon watanni biyu a duk fadin kasar.

Kakakin kamfanin na DisCos Mr. Sunday Oduntan shine ya sanar da hakan jiya laraba, inda ya kara da cewa kamfanin yayi la’akari da halin kalubale da wannan annoba ta Coronavirus ta ke haifarwa ga tattalin arziki da kuma halin rayuwa ta yau da kullun ga al’umma.

Ya kara da cewa “Muna bada hadin kai tare da bada gudummuwar mu ga matakan da gwamnati ke dauka na saukaka halin kunci ga ‘yan Nijeriya sakamakon wannan annoba ta Covid-19 ta hanyar daukewa ‘yan Nijeriya biyan kudin lantarki har na tsawon watanni biyu, biyo bayan takaitawa jama’a zirga zirga tare da zaman gida. Kuma nan bada jimawa ba zamu fayyace yadda zamu aiwatar da wannan shiri.

Kamfanin na DisCos ya kuma jinjinawa kokarin majalisar dokoki da majalisar zartarwa da kuma hukumar sa ido kan wutar lantarki ta kasa bisa ga yadda suka himmatu wajen ganin an samarwa ‘yan Nijeriya wutar lantarki yadda ya kamata a cikin wannan mawuyacin hali.

 Kamfunnan na wutar lantarki su kuma sun bada tabbacin samar da wutar lantarkin yadda ya kamata a duk tsawon lokacin wannan annoba ta Coronavirus.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 1