Coronavirus: Gwamnati ta Umurci a Rufe Jami’o’i  da Makarantu a duk Fadin Kasar.

Coronavirus: Gwamnati ta Umurci a Rufe Jami’o’i da Makarantu a duk Fadin Kasar.

Daga Mohammed Lawal :                                                                                    

Ma’aikatar ilimi ta tarayyar Nijeriya ta ba umurnin a rufe dukkan Jami’o’i da makarantun Sakandare da na Primary dake fadin kasar ba tare da bata lokaci ba, a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar Coronavirus.

Babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayyar Nijeriya Mr. Sonny Echono, wanda ya tabbatar da hakan, ya kara da cewa ministan ilimi na Nijeriya Malam Adamu Adamu, ya umurci shugabannin makarantun sakandare na gwamnatin tarayya su 104 dake fadin kasar da su gaggauta kammala jarabawar zangon karatu na biyu ga dalibai domin  rufe makarantun har sai abinda hali yayi.

Hakanan kuma ministan ya umurci shugabannin makarantun sakandaren na gwamnatin tarayyar da su samar da kayan tsabtace jiki kamar su sidarin wanke hannuwa ga dalibai domin samar da ingantaccen yanayi na kare yaduwar wannan cuta ta Coronavirus.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0