Buhari Shugaban Nijeriya Baki Daya, ba na Arewacin Nijeriya ba- Inji Shango.

Buhari Shugaban Nijeriya Baki Daya, ba na Arewacin Nijeriya ba- Inji Shango.

Daga Mohammed Lawal.

Shugaban taron majalisar dattawa masu kishin Nijeriya (PRONECO)Honorable Simon Shango ya maida martini ga shugaban kungiyar dattawan arewa (NEF) Farfesa Ango Abdullahi bisa ga wata wasika da Farfesa Ango ya rubuta, inda a ciki ya caccaki gwamnatin Buhari cewa gwamnatinsa ta gaza, musamman a yankin arewacin Nijeriya inda talauci da rashin tsaro sukayi kamari.

Chif Simon Shango ya janyo hankalin Farfesa Ango Abdullahi kan wadannan kalamai, inda ya bayyana cewa shugaba Buhari, ba shugaban arewacin Nijeriya ne ba, shugaban Nijeriya baki daya.

 A cikin jawabinsa amadadin kungiyar ta PRONECO, Chif Shango yayi watsi da ikirarin Farfesa Ango, inda ya bayyana shi a matsayin marasa tushe ko makama, musamman idan akayi la’akari da irin halin da shugaba Buhari ya iske Nijeriya a ciki, a lokacin da ya hau kujerar shugabanci, wato hali na matsanancin talaucin da koma bayan tattalin arziki gami da dimbin bashin da jihohi ke ciki.

Ya kara da cewa tun lokacin da shugaba Buhari ya karbi shugabancin kasar a shekara ta 2015, ya bullo da manufofi da shirye shirye da dama kan bunkasa tattalin arziki da tsaro.

 Chif Shango yace Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana son zuciya da rashin hangen nesa gami da rashin sanin ya kamata, a matsayinsa na dattijo, wanda ya kamata bada gudummuwarsa wajen ci gaban kasa maimakon yin kalamai na kiyayya ga wannan gwamnati

 Amma duk da haka, Chif Shango bai yi kasa a guiwa ba wajen bayar da shawara ga Farfesa Ango da ya guji yin batanci ga wannan gwamnati wadda take ta fadi tashi wajen ganin ‘yan Nijeriya sun ci moriyar dimukradiyya.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0